NASIHAR BUHARI GA ‘YAN MAJALISA TARAYYA: Duniya na kallo ku na zubar wa Najeriya mutunci

0

A cikin wani yanayin na ban-tausayi, Shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci ‘yan Majalisar Tarayya da su daina tozarta Najeriya a lokacin da duk duniya ke kallon abin da ke gudana a zauren Majalisar.

Hakan ya biyo bayan cin fuskar da Buhari ya fuskanta da kuma tozarta shi da wasu mambobi suka yi, a lokacin da ya ke gabatar da kasafin kudi na 2019.

An rika yi masa iho da sowa da furta ba ma yi, ba mayi. Wasu ma sun rika wuce gona da iri, su na cewa karya ce.

A cikin tattausar zuciya, shugaba Buhaeri ya roki mambobin da su daina abin da suke yi, domin duniya gaba daya na kallon abin da ke faruwa.

Buhari ya shaida musu cewa wannan ne kasafin kudi na karshe da zai gabatar wa majalisar a wannan zango na sa.
Ya dai sake tsayawa takarar shugabancin kasa a karo na biyu, wanda idan bai yi nasara ba, wannan ne zai kasance kasafi na karshe da ya gabatar a zauren majalisar.

A baya ya gabatar da na 2016, 2017, 2018 da kuma na yau, 2019.

MUN FUSKANCI KALUBALE A SHEKARU UKU BAYA

Buhari ya tabbatar musu da cewa a sheakaru uku da suka gabata, Najeriya ta fuskanci babban kalubale, amma kuma tattalin arzikin ya fita daga cikin halin kaka-ni-ka-yi da kasar nan ta tsinci kan ta.

Ya yarda da cewa wasu ayyukan ci gaban da aka kasa gudanarwa ya faru ne dalilin matsalar tsaro a cikin kasar nan.

ZA MU KAWAR DA MATSALOKIN BOKO HARAM DA RIKICIN MAKIYAYA DA FULANI

Duk da dai ya na magana ana karyata shi, Buhari bai daina furta inda kasar nan ta sa a gaba ba, har ya ci gaba da bayanain cewa an dauko hanyar magance matsalar makiyaya da kuma manoma da rikicin Boko Haram.

HALIN DA ASUSUN NAJERIYA KE CIKI

Shugaba Muhammadu Buahri ya shaida cewa a hanlin yanzu, lalitar Najeriya ta kasashen ketare adadin ta ya kai dala bilyan 42.92 ya zuwa cikin wannan wata na Disamba, 2018.

Ya ce amma a sheakaru uku baya cikin Mayu, 2016 adadin kudin da ke cikin lalitar bai zarce dala bilyan 20.57 ba.

MAIDA HANKALI GA KAMMALA MANYAN AYYUKAN RAYA KASA

Cikin jawabin Shugaba Buhari, ya yi mahganar cewa gwamnatin sa ta maida hankali sosai wajen kokarinn ganin an kammala manyan ayyukan da gwamnatin ta sa a gaba ba a kai ga kammalawa ba.

Ya kuma bugin kirjin cewa babu wata jiha a dukkan fadin kasar nan da ba a gudanar da wani gagarimin ayyukan gwamnatinn tarayya a cikinn ta.

MATSAYIN KASAFIN 2018 DA YA GABATA

Buhari ya ce kasafin 2018 na shekarar da ya kamata, ya wuce amma ya bar kwantai din ayyuka. Ya ce daga cikin naira tiriliyan 9.2 da aka yin kasafi a shekarar 2018, naira tiriliyan 4.59 kacal aka kashe ya zuwa cikin watan Satumba, 208 da mun ke ciki.

Ya ce akwai ayyuka da kirdadon ragowar naira tiriliyan 6.84 da ba a kai ga cimma ba.

Sai dai kuma ya ce duk sauran kwantai din, an saka ayyukan a cikin kasafin 2019.

NA AMINCE DA KARIN ALBASHI

Shugaba Muahammadu Buhari ya shaida wa majalisa cewa ya amince da karin albashi wanda ake ta sa-toka-sa-katsi a kan sa.

Ya kuma ce nan ba da dadewa ba zai aiko da kudirin da ya ke so majalisa ta maida karin albashin ya zama doka. Sannan kuma zai kafa kwamitin da zai gano yadda za a rika samar wa karin albashin kudaden da za a rika tafiyar da tsarin.

Share.

game da Author