Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnati ta kafa karin asibitocin dake kula da matan da ake cin zarafin su daga asibitoci uku a jihohi uku zuwa asibitoci 11 a jihohi 11 a Najeriya.
Ya fadi haka ne a taron inganta hanyoyin kare hakkin mata a Najeriya da aka yi a fadar shugaban kasa a Abuja.
Osinbajo ya yi kira ga mutanen kasar nan cewa domin samun ci gaba ya zama dole a hada hannu don ganin an kare hakkunan mata.
Bayan haka Osinbajo yace gwamnati za ta hada hannu da duk hukumomin da ya kamata domin ganin dokar kare hakkin mata a Najeriya ya sami kafuwa na din-din-din.
Ya kuma jinjina wa goyan bayan da kasar ta samu daga babban bankin duniya,UN, UNFPA,WHO,PIND,USAID, kungiyar Save the Children, Women Afrika, Soar Initiative da sauran sun wajen ganin an kare hakkin mata a kasar nan.
A karshe jami’in UN Ketil Karlsen a nashi tsokacin ya ce a shirye suke domin mara wa Najeriya baya wajen ganin ta kare hakin mata.
Discussion about this post