Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta maida hankali wajen ganin an kirkiro hanyoyin da za ci gaba da tallafa wa masu dauke da cutar Kanjamau ba sai an jira Tallafi daga kasashen waje ba.
Aisha ta yi wannan kira ne a taron wayar da kan matasa game da cutar Kanjamau mai taken ‘Free to Shine Campaign against Childhood Aids’ da aka yi a Abuja.
Ta ce Najeriya na da dukiyar da idan ta yi amfani da su yadda ya kamata kowa a kasar nan zai ji dadi.
Aisha ta yi kira ga ma’aikatar kiwon lafiya da ta bude asusu wanda hukumomi kamar su babbar bakin Najeriya, Kamfanin mai na kasa (NNPC),Hukumar jiragen ruwa na kasa(NPA) da NIMASA za su rika zuba kudade domin kau da cutar Kanjamau a Kasar nan.
Bayan haka Aisha ta bayyana cewa ita da sauran matan gwamnonin kasar nan za su zage damtse wajen ganin sun inganta kiwon lafiyar mata da jarirai a kasar.
” Za kuma mu hada hannu da ‘Free to Shine Campaign against Childhood Aids’ domin ganin burin kawar da cutar kanjamau yayi nasara a kasar nan.
A karshe shugaban kungiyar matan dake dauke da cutar kanjamau Helen Aphan ta yi kira ga Aisha Buhari da ta agaza wa mata masu dauke da cutar musamman yadda da dama daga cikinsu basa samun magungunan cutar akai-akai.
Discussion about this post