A jerin kasashen da ta’addanci ya yi kaka-gida a duniya, a karo na hudu a jere, Najeriya ta rike kambun ta na kasa ta uku da ke fama da matsalar ta’addanci a duniya.
Tun dagac 2015 ne Najeriya ta ke kasa ta uku, har zuwa yau, 2018. Sai dai a cikin 2014 ta kasance a jerin kasashe ta hudu, a kididdigar wadda Kungiyar Kididdigar Ta’addanci ta Duniya, wato Global Terrorism Index ta ke gudanarwa tun daga 2015.
A wannan rahoto na baya-bayan nan da aka fitar jiya Alhamis, Iraq ce kasar da ta’addanci ya fi addaba, kuma ita ce ta daya tun daga 2014 har yau 2018.
Ita kuma kasar Afghanistan ta kasance ta biyu tun daga 2013 har zuwa yau 2018.
Kasar Syria da Libya ne na biyar da na shida a jere.
Sauran fitattun da ke cikin goman farko na kasashen da ta’addanci ya yi wa katutu, sun hada da Somalia ta shida, India ta bakwai, Yemen ta takwas, Egypt ta tara da kuma Philipines ta goma.
Sai dai kuma labari mai dajin ji dangane da ta’addanci a Najeriya, shi ne a cikin shekarar 2017, an samu raguwar yawan wadanda ake kashewa kamar yadda aka rika samu a shekaru uku da suka shude a jere.
Rahoton GTI ya ce idan aka yi la’akari da yadda aka samu kisan mutane har 5,950 a cikin 2014, to za a iya cewa an samu raguwar kisan jama’a sanadiyyar ta’addanci a kasar a cikin 2017, inda aka samu rasa rayukan jama’a 1,532.