Najeriya ce kasa ta 11 wajen yi wa mata auren wuri a duniya

0

Cibiyar hana Fifita jinsin maza kan mata na majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa Najeriya ce kasa ta 11 cikin jerin kasashen duniya 20 dake aurar da mata da wuri.

Jami’in UN Edward Kallon ya fadi haka a taron samar da hanyoyin da za a iya bi don ganin an dakile haka da aka yi a Legas.

Kallon ya bayyana cewa aurar da ‘ya macen da bata kai ta yi aure ba kan haddasa talauci, cutar yoyon fitsari da sauran matsaloli da kan sa a fada cikin muggan matsaloli musamman wadanda suka shafi tattalin arzikin kasa da lafiyar ‘ya mace.

Kallon ya kawo jerin kasashen da suke da wannan matsala kamar haka: Kasar Nijar ce ke kan gaba wajen aurar da yara tun basu kai a aurar da su ba, sai kuma kasashen Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya dake da kashi 68 bisa 100, Chadi kashi 67 bisa 100, Bangladesh kashi 59 bisa 100, Burkina Faso kashi 52 bisa 100, Mali kashi 52 bisa 100
Sudan ta kudu dake da kashi 52, Guinea kashi 51, Mozambique kashi 48, Somalia kashi 45, Nigeria kashi 43, Malawi kashi 42, Madagascar kashi 41, Eritrea kashi 41, Ethiopia kashi 40, Uganda kashi 40, Nepal kashi 40, Sierra Leone kashi 39, Jamhuriyar Kongo kashi 37 da Mauritania kashi 37 duk bisa 100.

A karshe ministan harkokin mata Aisha Abubakar a nata tsokacin ta bayyana cewa lalle ya kamata a kawo karshen yiwa yara mata auren wuri musamman yadda tun farko suke fama da matslolin nuna wariya da ake musu da fifita jinsin maza a kan mata tun suna kanana har su girma.

Share.

game da Author