Dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa ya kosa ya hadu da Buhari a muhawara.
Idan ba a manta ba ranar juma’a ne ‘yan takarar mataimakan shugaban kasa suka fafata a muhawara da aka yi a Otel din Transcorp dake Abuja.
Tun bayan kammala mahawarar mutane ke ta tofa alabarkacin bakunan su bisa ga yadda muhawarar ya kaya.
Sai dai kuma mintuna kadan bayan kammala muhawarar Atiku ya rubuta a shafin sa ta tiwita cewa mataimakin sa ya taka rawar gani matuka.
Atiku ya ce yadda mataimakin sa ya amsa tambayoyin da aka tambayeshi ya burge shi sannan ya burge ‘yan Najeriya.
” Peter Obi, ya nuna wa ‘yan Najeriya cewa yana da sani matuka game da abin da ke faruwa a kasar nan. Ina matukar alfahari da shi.
Atiku ya kara da cewa yanzu haka har doki yake gamuwar su da Buhari a filin muhawara.
Sai dai kuma har yanzu ba aji komai ba daga fadar shugaban kasa game da ko Buhari zai halarci wannan muhawara ko kuma ba zai halarta ba.
Wasu da dama sun yi hasashen cewa kila Buhari ba zai halarci wannan muhawara ba.