MOURINHO: Yadda Babban Dodo Ya Zama Babban Matsoraci

0

Mai horas da ‘yan wasan Machester United, Jose Mourinho ya fara sukuwa a kan manyan ingarman dawakai a duniyar kwallon kwafa, tun bayan da ya samu nasarar lashe Kofin Zakarun Turai a karkashin kungiyar kwallon kafa ta FC Porto, da ke kasar sa ta haihuwa, Portugal.

Wannan nasara ce ta sa shekara mai zuwa kungiyar Chelsea FC ta London, ta sayo shi da tsadar gaske, inda a shekarar 2005 ya sake nuna wa duniya cewa dama fa kashin turmi ban a wadan kare ba ne. Domin a waccan shekara sai da Mourinho ya kai wasa na kusa da na karshe.

Barin sa kungiyar Chelsea, Mourinho ya taka rawa a kungiyar Inter Milan ta Italy da kuma Real Madrid ta Spain, inda daga baya kuma ya sake komawa Chelsea na dan takaitaccen lokaci, kafin daga karshe kuma ya tafi kungiyar Manchester United, inda ya ke har yanzu.

Sai dai kuma za a iya cewa bai koma kungiyar Man U din da kafar dama ba, domin tun bayan komawar sa kungiyar ke kwasar buhun kunya, ta inda ragar kulob din ta koma kamar rayiya, wadda kowane karamin kulob na Ingila na samun nasara a kan sa.

A yanzu kungiyar Manchester dai ci-da-karfi ta ke yi, daga kulob din har Mourinho, karsashi da kwarjini, cika-ido da muhibbar da suke da ita, sai kara dusashewa su ke iya a idon magoya bayan kungiyar a Ingila da ma duniya baki daya.

A yanzu fa idan har Mourinho na so ya tsira da mutuncin sa a wannan kakar wasa, to tilas sai ya samu nasarar wasanni na gaba fiye da kungiyar Tottenham da Arsenal da ma sauran masu hankoron shiga gasar Zakarun Turai na shekara mai zuwa.

Ba nasarar wasanni kadai ne kalubalen da ke gaban Mourinho ba. Tilas sai ya rika tala leda da kyau a cikin armashi yadda zai rika burge dimbin masoya kulob din, ba a rika yin harbatta-Mati ba.

Sannan kuma sai ya gyara dangantakar sa da ‘yan wasa da dama, musamman ma Paul Pogba, wanda Mourinho ya kira da cewa ‘ya zame wa Man U cutar sankara’, kwanan nan bayan sun tashi wasan tsakiyar mako da ci 2:2 da kungiyar Southamton.

A irin yadda Mourinho ke mu’amala da jama’a, musamman ‘yan jarida, akwai matsala a gaban sa matuka. Amma babbar matsalar sa ita ce yadda a yau zai karke da kungiyar Arsenal wadda dan wasan ta Aubegmiyang ke kan gaban neman zama zakaran da ya fi jefa kwallaye a gasar wasan Premier na bana.

Wasannin da Mourinho ya buga a baya-bayan nan duk bahallatsa ce kawai, haka ita ma Man U, bai kamata a ce a matsayin ta na namijin kura ba, a ce har gurgun mage na korar ta.

Kusan Mourinho da Gordiola a lokaci daya suka je Man U da Man City. Amma a zaman yanzu, maimakon Mourinho ya rika goyayya kafada da kafada da Man City, wadda ke ta daya, sai kokarin neman tarad da Everton ya ke yi, wadda ita ce ta shida a jerin Premier League.

Wani karin bambanci tsakanin Mourinho da Gordiola, shi ne, Gordiola ya san inda zai kashe kudi tsababa ya sayi dan wasan da bukatar sa za ta biya. Amma shi kuwa Mourinho, zuwan sa Man U ya rika rika yi wa kasuwar ‘yan wasan kwallo zaben-tumun-dare.

Kowa ya sa na yanzu tusa ta fara kare wa budarin Mourinho. Tun ya na jin tsoron manyan kulob, har ya fara fargabar kafsawa da kanana, kuma har ma ta kai shi ga tsoron tunkarar ‘yan jarida. Sai ka ce ba su da ‘yancin tambayar sa halin da kungiyar sa ke ciki.

Mourinho dai a yanzu ba ya takama da komai, ba ya takama da kuob din sa Man U, sai dai tutiyar a da su ne wane da wane. Sai bugun kirji da nasarorin sa na shekaru 10 ko sama da haka da ya samu a baya, ba a Man U ba.

Duk da Mourinho ya sake sabunta kwangilar sa da Man U, sai cikin 2020 zai kammala wa’adin sa, wawa ne kadai zai iya yankar caca ya zuba kudi ya ce Mourinho zai kammala wa’adin sa a kulob din.

Maimakon magoya baya su rika ganin Mourinho ya na warware musu damuwar su a cikin filin kwallo, sai ya shagala ko ya gafala wajen warware musu ita a shafukan jaridu, inda ya fi nuna gwanittar yadda zai yi nasara idan wasa na gaba ya zo.

Maimakon Mourinho ya rika karfafa wa ‘yan wasan sa guiwa kafin wasanni da kuma bayan kammala wasa, sai ya fi karkata wajen cin zarafin su da muzanta su a kafafen yada labarai.

Sai dai ganin sa suka yi ana hira da shi a wani gidan talbijin ya na cewa kokarin su dai shi ne su tabbatar da ba su wuce na shida sun kai na bakwai ba. Cewa fa ya yi “sai dai wata mu’ujiza daga Ubangiji kawai za ta iya sawa Man U ta iya yin ko da na hudu a kakar wasan Premier League na wannan shekara da ake gwabzawa yanzu.”

Wasu batutuwan da suka shafi ‘yan wasan sa ma sai a kafafen yada labarai suke karantawa, maimakon ya tunkare su ya bayyana musu.

Jama’a ya ku ke jin ‘yan wasa irin su Anthony Martial, Marcus Rashford, Luke Shaw da Jessi Lingard za su ji a lokacin da suka karanta wata hira da aka yi da shi a wata jarida inda ya ce musu karan hankalin su na kammalallun mutane bai kai tsaiko ba?

A shekarun baya, ko kungiyar kwanllon kafa ta ‘Yuyuyu FC’ aka ba Mourinho, cikin kankanin lokaci zai iya cin kowane kulob na duniya da wadannan ‘yan wasa.

A yanzu kuwa babu wata karamar kungiyar kwallon da ba za ta iya nasara a kan Mourinho ba. Sai fa idan ba a hadu an kafsa ba.

Shin ko ya zai karke da kungiyar Arsenal a daren yau din nan Laraba?

“Mu na ji, mu na gani, mu na kuma saurare!” Inji Shata, a cikin Gagarabadau.

Share.

game da Author