Ministan matasan da zan nada ba zai wuce dan shekaru 30 ba’ -Atiku

0

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar APC, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan ya ci zaben 2019, wanda zai nada a matsayin ministann harkokin matasa, ba zai shige sma da mai shekaru 30 a duniya ba.

Atiku yayi wannan bayani ne a lokacin da ya ke ganawa a matasa a wani zauren ganawa da matasan a Lagos, jiya Litinin.

Ya ce lokaci ya yi da shugabannin yanzu za su rika jan matasa a jika, kuma su na raino, kaynkayashewa da yaye matasa.

Daga nan sai ya kara da cewa ta hanyar da za a fi yin nasara a hakan kuwa shi ne ta hanyar shigar da matasa a cikin manyan mukaman gwamnati.

Atiku ya ce daga nan ne za su fara kuma su rika koyon tafiyar da mulki.

Ya kuma yi alkwarin cewa idan aka zabe shi ya zama shugaban kasa, to kashi 40 bisa 100 na gwamnatin sa, duk za su kasance mata da matasa ne.

Ya kara da cewa ya san yadda ake farfado da tattalin arzkin da ya durkushe. Ya kuma san yadda ake kirkiro ayyuka a cikin kasa, kuma ya san yadda ake inganta rayuwar matasa. Dalili ma kenan ya je Lagos domin ya baje wa matasan tsarabar da ya tanadar musu kowa ya gani, idan har ya yi nasarar zama shugaban kasa a zaben 2019.

Share.

game da Author