Karamin Ministan Harkokin Noma, Heiniken Lokpobiri, ya dora alhakin sumogal din shinkafa da ake yawan yi a cikin Najeriya a kan tsarin safarar kasuwanci tsakanin kasashen Afrika ta Yamma, wanda kungiyar ECOWAS ta shifimda.
Tsarin wanda ya bayar da dama gad an kowace kasa na Afrika ta Yamma na da ‘yancin shiga kowace kasa a cikin wannan yanki na Afrika ta Yamma ya sayo ko ya sayar ba tare da tsauraran sharudda ba.
Lokpobiri ya ce wannan tsari ya bai wa kasar Jamhuriyar Benin musamman damar bayar da kofa ana shigo da shinkafa daga kasar.
Ya ce tsarin ya na azurta Jamhuriyar Benin, a daya gefen kuma ya na illata shirin inganta noman shinkafa da gwamnatin Muhammadu Buhari ta fantsama ta na aiwatarwa a fadin Najeriya.
Dama cikin watannin da suka shige PREMIUM TIMES ta bayar da cikakken rahoton yadda ake shigo da shinkafar Thailand da ta Vietnam daga kan iyakar Benin ba kakkautawa a cikin Najeriya.
Musamman an gano cewa harkar sumogal din shinkafa ta tashi daga kan iyakar Seme ta koma kacokan a kan iyakar Badagry da Benin.
Lokpobiri ya yi wannan jawabin a lokacin da ya ke karbar sabon wakilin Hukumar Inganta Harkokin Noma ta duniya, wato IFAD a Abuja, wanda aka turo Najeriya.
Ya ci gaba da kokawa cewa Benin ta na kyale kasashe irin su Taiwan suna jibge shinkafa a kasar ta, sannan a sake dura su cikin sabbin buhunna a rika kwararosu cikin Najeriya.
Ya yi tsokaci ga Jamhuriyar Benin cewa wannan tsarin ko-in-kula da kasar ke yi, ya hana ta inganta noman shinkafa a cikin Benin din ballantana har kasar ta samu damar inganta harkokin noma.
Ya yi nuni da cewa kuma Najeriya ta mika wannan koke na ta har ga shi kan sa shugaban kasar Jamshuriyar Benin.
Discussion about this post