Kungiya mai zaman kanta ‘MedicAid’ ta bayyana cewa ta dauki nauyin kula da masu fama da cutar daji 600 a Najeriya.
Shugaban kungiyar kuma uwargidan gwamnan jihar Kebbi Zainab Bagudu ta bayyana haka a taron inganta aiyukkan kula da masu fama da cutar daji da kungiyar ta yi a Abuja.
Zainab ta kara da cewa MedicAid ta yi wa mutane 30,000 gwajin cutar daji a jihar Kebbi.
Bayan haka Jami’in kungiyar Ibrahim Hyelakumi ya yi kira ga mutane da su guji cin kitse, naman sa, alade, shaka da zukar taba domin guje wa kamuwa da cutar dajin dake kama dubura da ‘ya’yan maraina.
Ya ce nan ba da dadewa ba kungiyar za ta shirya taro da ma’aikatar kiwon lafiya domin ganin an inganta aiyukkan kula da masu fama da cutar daji a Najeriya.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa an karo na’urar kula da masu fama da cutar daji a babbar asibitin kasa dake Abuja.
Adewole ya fadi haka ne a ziyarar aiki da ya kai asibitin. Wannan shine na’ura na biyu da aka samar wa asibitin.
Ya bayyana cewa kamfanin SNEPCO ne ta tallafa wa asibitin da wannan na’ura sannan na’urar na da karfin kula da masu fama da cutar daji 100 a duk rana.
Adadin yawan irin wannan na’ura na warkar da cutar daji da Najeriya ke da su kaf guda takwas ne kuma ma wasu daga ciki basu aiki saboda tsufa da rashin kula.
Karancin na’urar ya kan sa mutane da dama dake fama da cutar fita zuwa kasashen waje domin samun kula sannan wadanda basu da karfin haka kan rasa rayukan su.
A karshe Adewole yace gwamnati na iya kokarin ta wajen ganin ta rage farashin samun kula domin talakawa su iya samu.
Sannan shugaban asibtin Jeff Mohmoh ya bayyana cewa asibitin na da ma’aikata da suke da kwarewa a wannan fanni.
Discussion about this post