MATSANANCIN YUNWA: Kananan yara 132 ne suka rasu a jihar Kaduna

0

Jami’ar kula da ciyar da yara abinci mai gina jiki, na jihar Kaduna Hauwa Usman ta bayyana cewa yara 132 ne suka rasu a dalilin matsananncin yunwa da suka yi fama dashi a jihar.

Jami’a Hauwa ta ce wadannan yara na daga ciki 12, 858 suka yi fama da hakan a shekarar 2018.

Hauwa ta fadi haka ne a zama da kungiyoyin ‘Children International (SCI)’ da ‘Civil Society Scaling-Up Nutrition in Nigeria (CS-SUNN)’ Suka yi a garin Kaduna.

Hauwa ta ce daga Cikin yara 12,858 din da suka yi fama da yunwa 10,604 sun warke sannan 132 Suka rasu.

” Bincike ya nuna cewa kashi 58.7 na yara ‘yan kasa da shekara biyar na fama da yun wa a jihar.

Hauwa ta ce haka na da nasaba da narashin maida hankali da wasu iyaye ke yi na rashin ciyar da ‘ya’yan su abincin da zai gina musu jiki.

A karshe jami’in CS-SUNN Silas Ideva ya yi kira ga gwamnatin jihar kan ware kudade domin kawar da Wannan Marsala.

Ya kuma yi kira ga kungiyoyi masu zaman kan su da hada hannu da gwamnati wajen ganin an tsara hanyoyin kawar da wannan Matsala tare da wayar da kan mutane game da illolin barin ‘ya’yansu cikin yunwa.

Share.

game da Author