Matsalolin Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi a Jihohin Arewa: Ina Mafita? Daga, Dr Mainasara Yakubu Kurfi

0

Babu shakka matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihohin arewacin Najeriya babban abu ne wanda ya dade yana ci ma al’umma tuwo a kwarya. Shekarun da suka gabata, matashi ko matashiya ba zasu yadda su bari a gansu suna shan miyagun kwayoyi ba saboda abun Allah wadai ne a idanuwan al’umma. Asali ma, idan aka ga mutum cikin maye akan bishi da waka da jifa ana: “tayi marisa, tasha kafso”.

Amma yanzu abun ya canza salo ta yadda matasa kan dauka cewar shan miyagun kwayoyi ado ne a wajensu. Har ta kai ana ganin wanda baya sha a matsayin wanda bai waye ba.

Bisa ga bincike-bincike da nazarorin masana da dama sun gano cewar abubuwa da dama kan haddasa jefa matasa cikin ta’ammali da miyakun kwayoyi. Wadannan abubuwa sun hada da: rashin aiki da talauci da rashin tarbiyya da sangartarwa daga iyaye da shiga matsanancin hali na rayuwa da sauransu.

Wadannan dalilai da wasu da dama na daga cikin dalilan da matasan da suka samu kansu cikin wannan hali na shaye-shayen miyagun kwayoyi ke bayyanawa a matsayin dalilan shiga yanayin da suka samu kansu.

Wadannan kwayoyi da suka hada da tabar wiwi da tiramol da sirof da bula da sholusha da shisha da kashin kadangare da kafso da dai sauransu na sa a shiga munanan halaye kamarsu tabin hankali, rama, rashin natsuwa da aikawa munanan halaye irinsu sace-sace, da fyade da rashin ganin girman kowa da mutunci cikin al’umma. Ba shakka, wadannan matsaloli na kawo rashin ci gaba ga matashi ko matashiyar da ta tsinci kanta a cikin wannan hali.

Hakkin iyaye ne da malaman makarantar muhammadiyya da ta boko da sauran al’umma su tashi tsaye wajen tarbiyantar da yara da matasa tun daga gidaje da makarantu da kuma cikin unguwanni. Tunda Hausawa kance: “tarbiyya daga gida takan fara”. Haka kuma, wajibi ne ga iyaye su dage wajen lura da shige-da-ficen ‘ya’yansu tare da lura da irin abokan da suke mu’amulla dasu.

Wajibi ne matashi yayi nazari sosai wajen lura da irin abokan da yake mu’amulla dasu. Bin Magana da shawarwarin iyaye wajibi ne ga matashi ma dammar yana son ci gaban rayuwarsa da zaman lafiya. Haka kuma, maida hankali wajen neman ilimin addini da na boko wajibi ne. Maimakon yawace-yawace a layuka da lungunan unguwanni, neman sana’a maimakon zaman kasha wando abu ne mai kyau ga matashi.

Daga karshe, hakkin gwamnatoci ne na tarayya da jihohi da kananan hukumoni da sauran hukumomin tsaro wadanda suka hada da na ‘yansanda, jami’an hana sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi su dage wajen wayar wa matasa kawunansu game da illolin shan miyagun kwayoyi da yadda suke haddasa tabarbarewar tarbiyya a cikin al’umma. Haka kuma ya kamata hukumomi su sa ido sosai wajen ganowa, kamawa da hukunta masu safara da sayar da irin wadannan kwayoyi a cikin al’umma.

Yana da kyau al’ummomi a cikin unguwanni su kafa kungiyoyin sa ido wajen ganowa da mika duk matashin da aka kama yana irin wadannan halaye na shaye-shayen kwayoyi ga hukuma domin hukuntawa. Wajibi ne matasa su san cewar idan suka saka kansu cikin wannan hali, tarbiyarsu zata gurbata, idan tarbiya ta gurbata zata shafi al’umma, idan ta shafi al’umma zata kawo rashin ci gaba a kasa.

Dokta Mainasara Yakubu Kurfi, Sashen Koyon Aikin Jarida, Jami’ar Bayero, Kano
mykurfi@gmail.com

Share.

game da Author