Kungiyar matasa ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan yin amfani da matasa wajen wayar da kan mutane game da mahimmancin amfani da dabarun tazarar iyali.
Kungiyar ta yi wannan kira ne a taron inganta hanyoyin samar da dabarun bada tazarar iyali da cibiyar DRPC ta shirya sannan ta gudanar a babban birnin tarayya, Abuja.
Shugaban kungiyar Lilian Anyanwu ta bayyana cewa kashi 47 bisa 100 na adadin yawan mutanen kasar nan matasa ne wanda ke ganiyar haihuwa kuma ke bukatan dabarun bada tazaran iyali.
Ta ce sai dai hakan ba shine ke samuwaba domin da dama na fama da matsalolin nuna wariya daga mutane musamman ma’aikatan kiwon lafiya sannan da matsalolin addini da al’adu.
” Wayar da kan matasa game da mahimmancin dabarun bada tasarar iyali musamman a makarantu da kuma hana ma’aikatan kiwon lafiya nuna wariya zai taimaka matuka.
Ta kuma yi kira ga matasa da su nemi bayanai daga wajen kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya a maimakon sauraron shawarwari daga wajen abokai.
Bayan haka Gidauniyyar Bill da Melinda Gates ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara yawan kudaden da take ware wa fannin kiwon lafiyar kasar domin samar da kiwon lafiya mai nagarta ga mutanen kasar.
Jami’ar gidauniyyar Paulin Basinga ta bayyana cewa yin hakan zai taimaka wajen karkato da hankalin gwamnatin kasar wajen inganta kiwon lafiyar mutane da hana kasar yawan dogaro da tallafin da take samu daga kasashen waje musamman yanzu da suka fara janye tallafin.
” Sanin kowa ne cewa idan ana so kasa ta ci gaba dole sai kasar ta sami shugabanin masu kishi da za su tabbatar cewa mutanen su na samun kiwon lafiya mai nagarta da kuma ilimi.
A karshe Basinga ta ce samar da dabarun bada tazarar iyali zai taimaka wajen kawar da matsalolin da mata da kuma jarirai kan fuskanta na yawan mace-mace a wasu lokutta da dama saboda rashin kula da ba a baiwa fannin kiwon lafiya.