Masarautar Kano za ta nada Naziri mawakin Sarkin Kano Sanusi

0

Kamar yadda duk wani mai bibiyar mawakar yankin Arewa a wannan zamani ya sani cewa shahararren mawakin nan, Naziru Ahmad ya maida hankali matuka wajen rerawa sarkin Kano Muhammadu Sanusi II waka tun nada shi Dan-Majen Kano a lokacin da yake gwamnan Babban Bankin Najeriya.

Yanzu hakar Naziru ta cimma ruwa domin kuwa masarautar Kano ta sanar da yi masa nadin sarautar mawakin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi.

Kamar yadda sanarwar ya fito daga fadar sarki Sanusi, za a yi bukin nadin ne ranar 27 ga watan Disamba.

Share.

game da Author