Masarautar Deba ta nada mata 5 sarautu dabam dabam a fadar mai martaba sarkin Deba Ahmed Usman.
Wadanda aka nada sun hada da Fatima Mohammed da aka yi wa sarautar Garkuwan Matan Deba sai Aisha Muhammed a matsayin Annurin Deba.
Sauran sun hada da Halima Muhammed, Tauraruwan Deba; Kulu Tela-sidi, Wakiliyan Matan Deba; da Abu Gurkuma a matsayin Sarkin kudun Deba.
Sarkin ya bayyana cewa jajircewar, kwazo da ayyukan gyara kasa ne da matan suke yi yasa masarautar ta karrama su da wadannan sarautu