Majalisar Dattawa ta tafi hutun karshen shekara

0

Majalisar Dattawa ta tafi hutun karshen shekara, kwana daya bayan zaman gambizar da ta yi da Majalisar Tarayya inda suka saurari jawabin kasafin kudi daga Shugaba Muhammadu Buhari.

An rufe majalisar ce yau Alhamis, 20 Ga Disamba, kuma sai ranar 16 ga Janairu, 2019 sannan za su koma a ci gaba da zaman majalisar.

Shugaban Masu Rinjyaye Ahmed Lawan ne ya karanto kudirin neman a tafi hutun, kuma aka amince.

Da ya ke jawabi, Sanata Lawan ya gode wa ma’aikatan majalisar, ‘yan jarida da sauran su, saboda gagarimar gudummawar da suka bayar wajen samun nasarar majalisar.

Sanata mai wakiltar Babban Birnin Tarayya da kewaye, Tanimu Aduda ne ya goyi bayan kudirin kuma aka amince da shi.

Mataimakin Shugaban Majalisa, Ike Ekweremadu, ya gode wa kowa da kowa kuma ya yi fatan a yi bukukuwan Kirsimeti da na Sabuwar Shekara lafiya.

Share.

game da Author