MAI RABON GANIN BADI: Yadda jihar Zamfara ta gagari gwamnatin Buhari

0

Mutane da dama sun rasa ‘yan uwa da aminan su a dalilin hare-haren ta’addanci da Mahara ke kaiwa kauyukan jihar Zamfara.

Wannan salo na ta’addanci ya na neman ya gagari gwamnatin Najeriya domin a kullum wayewar gari sai kaji sanarwar ko anyi garkuwa da wasu ko kuma an far wa kauyuka.

Ministan tsaron Najeriya Mansur Dan-Ali dan asalin jihar Zamfara ne kuma ma a karamar hukumar sa ne hare-haren yafi yin tsanani.

Saidai kuma zaman sa na ministan tsaro baiyi wa jihar tasirin komai ba domin kuwa duk da zaman sa haka ba a iya yin hubbasan ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar ba.

Abin takaici ma shine yadda a karamar hukumar sa ne wato karamar hukumar Birnin Magaji wannan ta’addanci yafi yin tasiri inda a kusan kullum sai kaji an fatattaki mazauna wani kauye dake jihar.

Akwanakin baya, minista Dan-Ali ya bayyana cewa rashin iya mulki na gwamnan jihar ne wato Abdul-Aziz Yari ya sa wannan ta’addanci yaki ci yaki cinyewa. Ya zargi gwamnan da nuna halin ko-in-kula da yake yi game da tsaron jihar da mutanen ta.

Sai dai kuma kafin nan shi kan sa Abdulaziz Yari ya jingina wannan matsala da jihar ke fama da ita ga wasu jiga-jigan gwamnati ‘yan asalin jihar dake Abuja.

Ya koka cewa sun hanashi sakat a jihar sannan sun suna amfani da kusantar su da Buhari suna cin karen su babu babbaka, mutane kuma a jihar na wahala.

Shi dai Yari ya sire wa matanen jihar kwata-kwata domin a kowani lokaci kayi kicibus da wani dan jihar Zamfara zai ce maka lallai ba su dace nagartaccen gwamna ba wannan karo.

Mutanen jihar su kan ce Yari bai dauke su da mahimmanci ba sannan kuma yadda ya ga dama ya ke yi a jihar. ” Shi dai Yari daga Abuja yake aikin sa, idan ma an kashe mu ba damuwar sa bane.” inji wani mazaunin jihar.

Kididdiga da aka yi ya nuna cewa akalla mutane sama da 3000 ne jihar ta rasa a dalilin ayyukan mahara da ta’addanci.

Kullum sai dai kaji wai an tura daruruwan jami’an tsaro amma kuma kisan ake yi babu kakkautawa.

” Mu dai a jihar Zamfara muna hannun Allah ne amma gwamnati ta gaza matuka. Yanzu ma bayan garkuwa da suke yi da mutane wanda sai an biya su ko kuma su yi kisa, sukan nemi yin lalata da mata idan suka far wa kauyuka. Bayan haka kuma su farfasa rumbuna su kwashi abinci yadda suke so sannan su kashe na kashe wa.

” Babu inda za a ce irin wannan tashin hankali na ta aukuwa kuma ace wai akwai gwamnati a wannan wuri. Mu dai mun zura wa ikon Allah ido ne kawai sannan muna ta addu’o’i.

Mun zuba wa Buhari ido ne domin tuni mun hakura muna da gwamna a jihar Zamfara sannan ko ministan tsaro da muke da shi dan asalin jihar bai tabuka komai ba akai, tunda sai dai kullum ace an turo amma a haka kuma ta’addancin sai dada yaduwa ya ke, ana kashe mutane kamar kiyashi, ana sace musu dukiyoyi.

Share.

game da Author