MAI RABO KA DAUKA: Atiku ya kaddamar da gasa ga ‘yan Najeriya game da yadda za a gyara Kasar nan

0

Dan takarar shugaban Kasa a inuwar Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya kaddamar da gasa ga duk yan Najeriya.

Shi dai wannan gasa za a yi shi ne a shafin yanar gizo in da za a dauki bidiyo game da yadda kake ganin yafi dacewa abi don gyara kasa Najeriya.

Shi dai wannan gasa mutum zai dauki kan sa ne a bidiyo sannan ya saka shi a shafin sa ta Facebook, inda daga nan masu bibiyar wannan gasa da alkalai zasu bi su duba sannan su bashi maki.

Wadanda aka fi yin muhawara a kan su sannan kuma suka fi bada ma’ana da mabiya guda 6 za a bayyana su sannan a saka su a gidajen Talabijin din kasa daga ranar 1 ga watan Janairun 2019 zuwa 6 ga watan.

Atiku ya ce wannan dama ce ya ba ‘yan Najeriya su fito su bayyana ra’ayoyin su game da yadda suke ganin ya fi dacewa a gyara Najeriya.

Atiku ya bayyana cewa ya yi haka ne domin kowani dan kasa ya bada gudunmuwar sa wajen ceto Najeriya daga matsalolin da take fama da su a yanzu.

Share.

game da Author