Wata mata mai suna Wandoo Daagu ta nemi kotun dake Makurdi da ta raba aurensu da mijinta Tertsea Daagu saboda babu sauran soyayya a tsakanin su.
Wandoo ta bayyana cewa ta auri mijinta ne a shekaran 2000 bisa ga sharudda na al’adun kabilar Tiv sannan sun haifi ‘ya’ya uku tare.
Ta ce tun bayan da ta haifi wadannan yara ne mijinta ya fara zarginta da kwana da maza a waje sannan a duk kwanan duniya sai ya lakada mata dukan tsiya.
” Da dai na ga bazan iya daurewa ba kuma sai na tattara nawa-inawa na koma gidan iyaye na sannan tun da na koma Daagu bai turo magabatan sa ba domin a sassanta mu.
Wandoo ta roki kotun da ta raba auren su saboda ta ce yanzu babu sauran soyayya a tsakanin su.
Shi kuwa Daagu ya karyata duk hujjojin da matarsa Wandoo ta fada a kansa a kotu.
Ya ce matarsa Wandoo ce ke kwana da wani limamin cocin su na NKST.
” Duk da haka sai na hakura na yarda na ci gaba da zama da ita a matsayin matata. Sannan a wannan lokacin babu Zagi ballantana duka da ya taba hada mu.
” Haka kawai bayan shekara daya sai Wandoo ta tattara nata-inata ta koma gidan iyayen ta da zama tare da goyan bayan iyayen ta sannan ni kuma an bar ni ba tare da nasan dalilin yin haka da ta yi ba.
Shima mijin nata ya amince kotru ta raba auren kowa ya huta.
A karshe alkalin kotun Adole Akintomide ya daga shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Disamba.