Mahara sun kashe mutane da dama a wasu kauyukan jihar Zamfara

0

Wasu mahara sun kashe mutane da dama a kayukan Garin Haladu, Garin Kaka da Nasarawa Godal dake karamar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara.

Birnin Magaji can ne mahaifar Ministan Tsaro, Mansur Dan-ali, kuma mahaifin sa ne Hakimin Masarautar Karamar Hukumar.

Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da baya so a fadi sunan sa ya bayyana haka wa PREMIUM TIMES ranar Alhamis.

Mazaunin yace maharan sun far wa kauyen Garin Haladu inda suka kashe manoma 12 a gonakin su da karfe daya na ranar Laraba.

” Da yamma kuma sai suka sake shiga wasu kauyukan dake kusa da wadannan kauyen inda suka kashe wasu mutanen kuma.

” A lissafe maharan sun kashe mutane 12 a Garin Haladu, hudu a Nasarawa Godal sannan a Garin Kaka suka kashe mutane tara.

Mazaunin yace a dalilin wannan hari da dama sun sami rauni a jikinsu sannan suna samun kulan da suke bukata a asibiti.

Bayanai sun nuna cewa wannan ba shine karo na farko ba da mahara ke kai wa kauyukan jihar Zamfara hari.

Hare-hare irin wannan ya hana mazaunan kauyukan Ballaka, Tsalle, Gidan Kare, Katsinawa, Garin Boka da Garin kaka sakat inda gaba daya sun koma hedikwatan karamar hukumar Birnin Magaji.

A yanzu dai kananan hukumomin da suke yawan fama da wannan matsalar sun hada da Tsafe, Zurmi, Shankafi, Maradun, Maru da Birnin Magaji.

Rundunar ‘yan sandan jihar batace komai ba game da harin.

Share.

game da Author