Wasu ‘yan Bindiga sun harbe tsohon babban hafsan sojojin Najeriya Alex Bade a hanyar sa ta zuwa garin Abuja daga Keffi, jihar Nasarawa.
Badeh ya rasu ne a dalilin harbin da ‘yan bindigan suka yi masa bayan ya fito gonar sa dake Keffi.
Rundunar Sojin saman Najeriya ta fitar da haka a shafinta ta Tiwita inda ta ke mika sakon jaje da ta’aziyyar ta ga iyalan marigayi Alex Badeh.