Magidanci ya roki kotu ta raba shi da matar sa gudun kada ya kashe ta

0

Franklin Temitayo mai shekara 50 kuma mijin Titilayo ya roki kotun dake Agege jihar Legas da ta raba shi da matar auren sa su gudun kada ya kashe ta wata rana.

Temitayo ya bayyana a kotu cewa matarsa Titilayo mafadaciya ce sannan bata girmama shi a matsayin mijin ta.

Ya ce shekarun su 14 tare da Titilayo amma kulum zaman su jiya i yau. Babu zaman lafiya.

” Da dan albashin da nake samu wurin aikina nake ciyar da iyalai na amma kulum matata bata ganin kokarina.

” Akwai ranar da Titilayo ta cukume mini kwalar riga saboda kudin abincin da ko da na bada shi ba ta ma siyan abincin.

Ita kuwa Titilayo ta karyata korafin da Temitayo ya fada game da ita a kotu.

” A cikin shekarar nan Temitayo ya sace ‘ya’yan mu bayan ya zo da sunan duba su a gida.

Titilayo ta roki kotu da ta sassanta su saboda bata so ‘ya’yan su taso ba tare da mahaifin su ba.

A karshe alkalin kotun Patricia Adeyanju ta hori ma’auratan da su sassanta kansu sannan ta daga shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Janairu.

Share.

game da Author