A ranar 28 ga watan Nuwamba likitocin dake aiki a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Enugu (ESUTH) suka fara yajin aiki domin nuna fushin su da bambamcin albashinsu da albashin likitocin dake aiki da ma’aikatar kiwon lafiya na jihar da gwamnati ke biya.
Shugaban kungiyar likitoci na kasa reshen jihar Enugu (NMA) Ike Okewesili ya bayyana haka inda ya kara da cewa gwamnatin jihar na biyan likitocin dake aiki da ma’aikatar kiwon lafiya fiye da likitocin dake aiki da asibitocin gwamnatin dake jihar.
Okewesili ya ce a dalilin yi musu kunen uwar shegun da gwamnati ta yi game da biyan bukatun ne ya sa suka fara yajin aiki.
” Kungiyar mu ta yi kokarin tattaunawa da masu fada aji ko kila gwamnati za ta ji tausayin mu ta fara biyan dai dai da liktocin ma’aikatar kiwon lafiya amma duk hakan bai yiwu ba.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta ruwaito cewa a dalilin yajin aikin da likitoci suka fara a asibitin ESUTH marasa lafiya da dama sun fice daga asibitin.
Wata ma’aikaciyyar jinya da bata so a fadi sunan ta ta bayyana cewa dole suka sallami marasa lafiya saboda karancin likitoci.
” Wadanda suka rage a asibitin sune wadanda cutar su ya yi tsanani. Ta ce.