Wasu daga cikin ginshikan al’adar Bahaushe ko Hausawa sun hada da kunya, kawaici da kara musamman a yayin mu’amala ko alaka da juna ko kuma da wasu mutane daga wasu al’adun.
Wadannan dabiu na Hausawa na bukatar sassauta harshe, jin nauyi ko bangirma musamman ga mutanen dake da wata daraja, matsayi ko mukami na mulki ko shekaru.
Wannan sune dalilan da yasa Bahaushe cikakke ke kasa aikata wani abu na masha’a a gaban wani babban mutum a shekaru ko matsayi. Haka kuma Bahaushe kan gaza cin mutunci, tozarta ko kuma wulakanta mutum kai tsaye ba kuma da kwararan dalilai ba saboda wadannan kyawawan dabiu na al’adar Bahaushe.
Bayan mulkin mallaka da turawan Ingila suka yiwa Najeriya da kuma cakuduwar al’adar Bahaushe da al’adar Bature tare da angizo, kururutawa da dabbaka tsarin mulkin Dimokaradiyya, sai al’adar Bahaushe ta fara canzawa daga asalin yadda take izuwa ta wasu mutane da fahimtarsu ta kara, kawaici da kunya ta banbanta da fahimtar Bahaushe.
Damokaradiyya tsarin mulki ne da ke bawa dukkan dan kasa da ya cika sharuddan zabe da ya zabi ko a zabeshi a shugabanci. Wannan tsarin mulki na tabbatar da yancin magana, mu’amala, cudanya da kuma adalci ga kowane mutum ba tareda tsangwama, kyara ko banbanci ba ta kowane fanni.
Wannan yanci ne yasa Bahaushe a tsarin Dimokaradiyya ke mantawa da kyawawan dabiu da al’adunsa wadanda ke sashi ganin mutunci, girma, daraja da daukaka ta mutane musamman manya ta yanda baya iya aibatasu ko kuma aikata wani abu na rashin kyautawa a gabansu.
Babu shakka za’a iya cewa kyawawan al’adun Bahaushe na kawaici, kara da kunya na kokarin gushewa a sanadiyyar tabbatar da mulkin Dimokaradiyya da sunan yancin fadar albarkacin baki. Abu ne mai sauki a yanzu ga Bahaushe yayi amfani da kafafen yada labarai kamar radiyo, talabijin, jarida, mujalla da kuma kafafen sadar da zumunta kamar facebook, twitter, instagram da whatsapp karara wajen aibata ko cin zarafin wani babban mutum a saboda dalilai na siyasa.
Haka kuma sau da dama Bahaushe kan iya fuskantar wani babban mutum a zahiri ya gaya masa ko fadin maganganu marasa dadi ko kuma aikata wani abun kunya, batsa ko abin takaici a gabansa ba tare da jin kunya ko kawaicin wannan mutum ba.
Babu shakka Dimokaradiyya tsari ne mai kyau da amfani musamman idan mukayi la’akari da wasu manyan kasashe da suka ci ribar tsarin wajen ci gaba da kuma samar da kyakyawan yanayi don ci gaba ga mutanen su. Wadannan kasashe sun hada da Ingila, Amurka da Jamus.
Saboda haka yana da kyau Bahaushe ya fahimci alfanu na Dimokaradiyya ya kuma san ta hanyar da zai ribaceta ba tare da wulakanta ko banzantar da kyawawan al’adun sa ba.
Hassan Alhaji Ya’u, Ph. D.
Department of information and media studies, Bayero University Kano.