Kungiyoyi uku sun nemi Buratai ya yi bayanin yadda ya kashe kudaden yaki da Boko Haram

0

Kungiyoyin Kasa, Kishin Tattalin Arziki da kuma ta Neman ’Yancin Bayyana Bayanan Gwamnati, sun rubuta wa Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Tukur Buratai wasika, inda suka nemi ya yi bayani dalla-dalla a rubuce, ta yadda ya kashe kudaden da aka ware masa domin yaki da ta’addanci daga 2015, 2016 da kuma shekarar 2017.

Kungiyoyin da suka hada da SERAP, sun nemi Laftanar Janar Buratai ya yi bayanin adadin kudaden da ya kashe daga 2015, 2016 da 2017 a kan Operation Lafiya Dole, Operation Safe Haven, Operation Pethon Dance, Operation Ruwan Wuta, Operation Mesa, Operation Harbin Kunama, Operation Tsare Teku da Operation Harbin Kunama.

Wadanda suka sa wa wasikar hannu sun hada da shugaban SERAP, Bamisope Adeyanju, Seun Akinyemi na da Atiku Samuel na BudgIT.

Sun ce fitowa a yi wa jama’a bayanai dalla-dalla zai warware abin da ya shige wa mutane duhu ta yadda za su daina tambayar yadda ake kashe kudaden.

Sun ci gaba da cewa idan har aka yi kwanaki 14 ba su ji bayanin komai daga Buratai ba, to za su maka Buaratai kotu domin a tilasta shi fitowa da bayanan.

Sun kuma ci gaba da cewa an kashe makudan kudaden wajen yaki da Bokon Haram, a tsakanin shekarun 2015, 2016 da 2017 masamman a yankin Arewa maso Gabas, amma babu wata alamar da ke nuna cewa kudaden da aka kashe sun kara wa sojojinmu kuzari da kumajin yaki sosai.

Bayan wannan sun kuma yi korafin cewa kudaden da aka kashe a yaki da Boko Haram ba su nuna alamar samun wani gagarimin ci gabaci gaba a yadda ake yaki da Boko Haram ba.

Share.

game da Author