A ranar Laraba ne shugaban kungiyar malaman Kwalejojin Kimiyya da Fasaha (ASUP) Usman Dutse ya bayyana cewa malaman za su fara yajin aiki daga ranar 12 ga watan Disamba.
Dutse ya sanar da haka ne da yake ganawa da PREMIUM TIMES ta wayar tarho inda ya kara da cewa ASUP ta yanke shawarar haka ne saboda rashin biyan bukatun malaman da gwamnati ta ki yi.
Ya ce tun a shekarar 2014 ne kungiyar da gwamnati suka sa hannu a takardar yarjejeniyyar biyan bukatun malaman kwalejojin dake kasar nan amma shiru kamar ba ayi ba har yanzu.
” Mun gaji da kai ruwa rana tsakanin mu da gwamnati kawai mun yanke shawarar mu shiga yajin aikin kawai in ya so daga baya a san abin da da za yi nan gaba.