Kotu ta sabule wa APC bangaren Amaechi wando a tsakiyar kasuwa

0

Kotun Daukaka Kara ta Musamman da Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Kasa, Zainab Bulkachuwa ta kafa, domin zartas da hukuncin rikicin da ya dabaibaye APC a jihar Ribas, ya kori karar da bangaren shugaban jam’iyya na jiha, Flag-Amachree Ojukaiye ya shigar.

Shugaban Kwamitin Alkalan, Abubakar Yahaya, ya zartas da hukuci jiya Laraba a Babbar Kotun Daukaka Kara da ke Fatakwal.

Kotun ta kara jaddadawa da amincewa cewa ba a gudanar da zabukan shugabannin jam’iyya a jihar ba, haka na kananan hukumomi da kuma mazabu na fadin jihar Ribas.

Wannan hukunci da aka yanke kuwa zai iya shafar zaben da aka yi wa na hannun damar Minista Rotimi Amaechi a matsayin dan takarar jam’iyyar APC na jihar Ribas, domin APC bangaren Ojukaiye ce ta shirya zaben da aka tsaida shi dan takara.

APC tare da daurin girndin su Rotimi Amaechi ta tafka kuskuren shirya zaben fidda-gwani, duk kuwa da cewa akwai hukunci daga Babbar Kotun Jiha cewa kada a shirya zaben har sai kotu ta yanke hukuncin.

Dama kuma a baya PREMIUM TIMES ta bayar da cikakken labarin yadda kotu ta yi watsi da zaben fidda gwanin jihar Ribas, wanda Tonye Cole ya yi nasara, saboda bangaren Sanata Magnus Abe ya kai karar cewa su Amaechi ba su shirya zaben shugabannin jam’iyya tare da magoya bayan sa ba.

Bayan wannan kuma sai kotu ta soke zaben ‘yan takarar sanata, na wakilan tarayya da na ‘yan majalisar dokoki da APC bangaren Amaechi ta shirya, ba tare da bayar da dama bangaren Sanata Magnus Abe sun shiga zaben ba.

Dukkan wadannan zabukan da su da na shugabannin jam’iyya, duk kotu ta ce haramtattu ne.

Share.

game da Author