Kotu ta ci gaba da tsare mai gadin da ya saci wayar wani alkali

0

Wata Kotun Majistare da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta bada umarnin a ci gaba da tsare Samson John da Ayodele Oluwagbemiga, bisa zargin su da ke yi da satar wayar alkali.

Mai Shari’a Ibijoke Olawoyin ce ta bayar da wannan umarnin a jiya Talata, bayan an gurfanar da wadanda ake zargin da aikata laifukan shiga wani gida ba da izni ba, karya kofar gidan da kuma dibga sata a cikin gidan.

Daga nan sai ya dage shari’ar zuwa ranar 20 Ga Disamba domin ci gaba da sauraren karar.

Tun da farko dai mai gabatar da kasa Alhassan Jibrin, ya shaida wa kotu cewa wani mai suna Usman Olayinka da ke kotun Basin a Ilorin ne ya kai kara a ofishin ‘yan sanda a Ilorin.

Ya shaida cewa wanda ake karar kuma mai gadin gidan, ya hada baki da wani suka saci wayar selula samfurin Samsun Galaxy wadda aka kiyasta kudin ta Naira 300,000 da kuma sarkar mata wadda kudin ta ya kai naira 10,000.

Ya ce an bi mai gadin har garin su Oputa da ke cikin jihar Benuwai, aka kamo shi.

Bayan an yi masa tambayoyi, y ace ya shiga dakin da ya yi satar ta hanyar yin amfani da makullin dakin bayan-gidan sa, ya bude dakin da ya yi satar.

Ya furta cewa ya sayar da wayar naira 10,000 kacal ga wani mai suna micheal da ke garin.

Sannan kuma kayan sarkar ya saida su ga wani da ake zargin su a yanzu tare, a kan kudi naira 7,000.

Sauran Micheal da ya sayi waya kuma ya cika wandon sa da iska.

Dukkan su dai sun ki amsa zargin tuhumar da ake yi musu.

Share.

game da Author