Wata Kotun Majistare da ke Jihar Osun da ke garin Modakeke, ta daure wani mai suna Jimoh Oyeyemoni tsawon shekaru uku a kurkuku saboda samun sa da aka yi da laifin yi wa tsohuwa mai shekaru 80 fyade.
Mai gabatar da kara Ona Glory, wadda Sufeton ‘yan sanda ce, ta shaida wa kotu cewa wanda akwe tuhumar ya aikata fyaden a ranar 23 Ga Disamba da misalin karfe 2:30 na rana, a kauyen Onibambu, kusa da garin Modakeke.
Ta ce Jimoh ya afka wa gyartumar mai suna Sogunlana ba tare da amincewar ta ba, a cikin gonar ta.
Ya yi barazanar zai murde mata wuya idan ba ta amince da shi ba.
Mai Shari’a A. O. Famuyide ya daure shi shekaru uku ba tara da ba shi zabin biyan tara ba, domin hakan ya zama ishara a gare shi da kuma sauran batagari irin sa.