Babbar Kotun Jihar Filato, a karkashin shugabancin mai shari’a Daniel Longji, ta bada belin mutane 20 da aka kama bisa zargin kisan Janar Idris Alkali mai ritaya.
An dai kama mutane 28 a cikin watan Oktoba, da laifin sace Janar din da kuma kashe shi tun a ranar 3 Ga Satumba da aka bada sanarwar bacewar sa.
Ya bace ne a lokacin da ya ke kan hanyar sa daga Abuja zuwa Bauchi, a kauyen Dura Du, cikin Karamar Hukumar Jos ta Kudu.
“Na saurari bangarorin biyu na mai shigar da kara da na mai kare wadanda ake kara. Dangane da batun beli, zan yi amfani da sashen doka na 100, 138 da na 148.
“Wannan sashe ya nuna cewa laifin da ake zargin su da shi na kin sanar da hukuma wani bayani, taro ba bisa ka’ida ba da kuma kin amincewa a binciki wanda ake nema a yankin su, duk laifuka ne da za a iya bayar da belin su.
“Da a ce ma an kama su da laifi, to da yanzu sun kammala wa’adin dauri a kurkuku.” Inji Mai Shari’a.
“Dangane da sauran wadanda ake zargin kuma, ba ni da lokacin da zan duba takardun bayanan karar ta su, saboda tuli ne guda masu yawan gaske. Sai bayan na yi nazarin su tukunna.”
Longji ya bayar da belin 20 daga cikin su 28 beli a kan kudi naira milyan daya kowanen su, tare kuma da mai tsaya musu, wanda zai kasance shugaban al’umma ne, kuma zai yi rantsuwa a kotu cewa duk ya san waanda ya karbi belin sa.
Ya aza ranar 25 Ga Janairu, 2019 domin sauraren batun bayar da belin sauran su 8 da suka rage a kurkuku.
Discussion about this post