Hukumar hana yaduwar zazzabin cizon sauro na kasa (NMEP) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ware kudade domin ganin an kawar da zazzabin cizon sauro a kasar.
Jami’in hukumar Audu Mohammed ya sanar da haka a taro da aka yi a Abuja.
Mohammed ya ce rahotan cibiyar ‘World Malaria Report’ na shekarar 2017 zuwa 2018 ya nuna cewa an sami akasi game da aiyukkan kawar da cutar da kasashen duniya ke yi daga shekarun 2017 zuwa 2018.
Rahotan ya nuna cewa a shekarar 2017 cutar ta yi ajalin mutane da yawa a kasashen Afrika da India.
Mohammed yace a dalilin haka yake kira ga gwamnati da ta zage damtse don ganin an dakile yaduwar cutar musamman yadda cutar ke yin sanadiyyar mutane da dama a Kasar nan.
” Muna kira ga asibitoci masu zaman kan su da su mara wa wannan shiri baya ta hanyar rage farashin magungunan cutar.
A karshe ya yi kira ga mutane da su rika tsaftace muhallinsu, su rika amfani da gidajen sauro musamman idan za a kwanta barci sannan mata masu ciki su dinga gwajin cutar domin samun kariya.
Discussion about this post