Kashi 1 bisa 3 na ’yan Najeriya duk jahilai ne – Inji Ministan Ilimi

0

Ministan Harkokin Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana cewa akwai kimanin jahilai da ba su iya karatu da rubutu ba a Najeriya kusan miliyan 60.

Adamu ya fadi haka ne a birnin Kano, jiya Laraba, inda ya ce wadannan jahilai da ya ke magana a kai, duk matasa ne da kuma magidanta.

Ya ce tunda an kiyasta cewa adadin ‘yan Najeriya sun kai miliyan 180, hakan kenan ya ne nufin kashi 1 bisa 3 na daukacin ‘yan Najeriya duk jahilai ne kenan.

Adamu wanda Mataimakin Darakta na Fannin Ilimin Firamare da Sakandare, Prince James ya wakilta a wurin taron, ya yi bayanin ne a taron shekara ta 2018 na murnar zagayowar Ranar Ilimi/Karatu/Rubutu ta Duniya.

Ya kara da cewa kashi 60 bisa 100 na marasa ilimin duk mata ne, yayin da Najeriya ta na da yara kanana har miliyan 11 wadanda ke watangaririya, ba su zuwa makaranta.

Ya ce akwai bukatar a gaggauta shawo kan wannan babbar matsala, ganin cewa Najeriya na hankoron cimma kudirin ta na kawar da jahilcin karatu da rubutu da rashin ilimin gaba daya nan da shekara ta 2030.

Share.

game da Author