Shugaba Muhamamadu Buhari ya bayyana cewa a cikin kasafin kudi na 2019, za a ware naira bilyan 305 domin biyan kudin tallafin farashin man fetur, wato ‘subsidy’.
Buhari ya bayyana haka a lokacin da ya ke karanta jawabin sa a zauren Majalisar Tarayya jiya Laraba.
Idan ba a manta ba, kafin hawan Buhari mulki, ya rika sukar gwamnatin Goodluck Jonathan da ta ke biyan kudin tallafin man fetur.
Buhari ya rika cewa sata ce karara da kuma damfara da ake rika biyan kudaden tallafin mai ga masu shigo da fetur daga wajen kasar nan.
Ya rika yin wannan furucin ne a lokacin da litar fetur ke naira 87.
A cikin 2016 ne Buhari ya soke tallafin man fetur. Wannan ne ya sa dukkan manyan dilolin da ke shigo da mai suka janye hannun su, suka ce sun daina, domin duk wanda ya shio da fetur, to faduwa kasar warwas zai yi, maimakon ya ci riba.
An bar kamfanin mai na gwamnatin tarayya, NNPC da nauyin shigo da tataccen man fetur ita kadai, sai dai kuma an kara tsawwala masa farashi, akan naira 145 kowace lita, maimakon naira 87 a lokacin mulkin Jonathan.
NNPC ta gano cewa duk da karin kidin man fetur da gwamnatin Buhari ya yi, ita kan ta idan ta sayo fetur tatacce daga kasashen waje, to ba zai saidu a kan naira 145 ba, sai dai a kan naira 185 kowace lita.
Ta ce farashin zai karu ne a cikin Najeriya zuwa 185 din, saboda biyan kudin saukalen fetur din daga jiragen ruwan da ke jigilar sa, da kuma kudin aikin jigilar raba man a cikin fadin kasar nan.
NNPC ta ci gaba da saida fetur a kan naira 145, wato ta na yin asarar naira 40 kenan a kowace lita daya ta fetur.
Dalili kenan NNPC ta rika cirar naira 40 daga kowace lita ta kudin Asusun Ribar Gas na Kasa, wato NLNG, ta na gabzawa a cikin rarar kudin man fetur da ta ke samu a kowace lita daya, har naira 40.
Ta rika yin haka ne a matsayin cike gibin naira 40 na kowace litar man fetur.
Wannan kudade ne da NNPC ta rika zara a boye ya haifar da rudani tsakanin gwamnatin tarayya da Majalisar Dattawa, wadda ta yi kakkausan korafin cewa ana cirar kudin a boye ba tare da sani ko amincewar Majalisar Dattawa din ba.
Su dai kudaden da ke cikinn asusun NLNG, kudade ne mallakar tarayya, johohi da kuma kananan hukumomi, wadanda
haramun ne a taba ko sisi a ciki ba tare da sani da kuma amincewar Majalisar Dattawa ba. haka dai dokar kasar nan ta shar’anta, kuma ta gindaya.
Majaliasr Dattawa ta gano cewa gwamnatin tarayya a karkashin NNPC, ta gabji har naira bilyan 320 a asirce daga asusun NLNG ta zabga a cikin asusun NNPC ba tare da sanarwa ba.
An yi ta kai ruwa-rana har dai daga karshe Shugaban Kamfanin NNPC, Maikanti Baru ya fito fili ya tabbatar da cewa tabbas an ciri dala biliyan 1.05 daga asusun NLNG an maka cikin na NNPC, wanda adadin kudaden sun yi daidai da naira biliyan 320 din da Majalisar Dattawa ta ce an kwasa.
Cirar wadannan kudade ya rika jefa jihohi da kananan hukumomi cikin halin kuncin kudade.
Majalisar Dattawa ta kafa hujjar cirar kudaden ne daga wani labari da jaridar PREMIUM TIMES ta fallasa, cewa gwamnatin Buhari ta cire kudaden a asirce, ba tare da sanin Majalisar Dattawa ba.
A yanzu dai Gwamnatin Buhari ta dawo da biyan tallafin mai, wato ‘subsidy’, bayan karin kudin fetur din da ta yi daga naira 87 zuwa naira 145.