Kungiyar Ma’aikata da aka fi sani da Kungiyar Kwadago ta Kasa, ta yi watsi da furucin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi cewa zai amince da karin albashi, amma za a sake duba batutuwan da ka iya tasowa bayan karin albashin.
A jiya ne dai Buhari ya bayyana a cikin jawabin kasafin kudi a Majalisar Tarayya cewa, zai turo da batun karin albashi a majalisa domin a amince ya zama doka.
Sai dai kuma a cikin jawabin na sa, Buhari ya nemi ‘yan majalisa da su bi batun a cikin tsanaki, domin su duba yadda karin albashin ba zai kara tsunduma Najeriya shiga gidaje ko kasashe neman ramcen kudaden da za ta rika biyan albashi a kowane karshen wata ba.
Wannan furuci na Buhari ne shugabannin kungiyar ta kwadago, suka yi wa kakkausar suka.
Sun jaddada cewa su kawai abin da suka sani shi ne, Shugaba Buhari ya sa hannun amincewa cewa naira 30,000 ce mafi kankantar albashi kawai, kuma ya mika wa majalisa ita ma ta amince, shikenan batun ya zama doka.
Sun ce ba za su yarda da duk wani bincike-bincike da kwakule-kwakulen yadda za a nemo mafita a nan gaba kamar yarda Buhari ya yi bayani ba.
Har ila yau, Buhari ya ce zai kafa kwamiti wanda zai gano hanyoyin da tsarin biyan albashin zai dore, ba tare da an rika kame-kame ba, kuma ba tare da ya haifar da tsadar kayan masarufi ko kuma haifar da korar ma’aikata daga aiki ba.
Shugaban Kwadago Ayuba Wabba, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN cewa duk wani sa-toka-sa-katsi da gwamnatin tarayya za ta yi, idan ta sake ta rage ko da naira daya daga cikin naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi, to ba za su taba amincewa ba.