Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa abinda ya dace shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi shine yayi murabus kawai bisa ga kalaman da yayi kan tattalin arzikin Najeriya
Idan ba a manta ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa taron gwamnonin Najeriya cewa kowa fa ya shiga taitayin sa domin tattalin arzikin kasar nan na cikin mawuyacin hali.
Buhari ya fadi wa gwamnonin ne a ganawar sirri da yayi da su a fadar shugaban kasa da yamman Juma’a.
Gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya bayyana wa manema labarai bayan kammala taron.
” Buhari ya fadi mana cewa kowa fa ya shiga taitayin sa domin tattalin arzikin kasa ya fada cikin mawuyacin hali yanzu.”
Sai dai kuma Yari bai yi bayani dalla-dalla ba bisa ga abubuwan da suka tattauna da shugaba Buhari ba bayan wannan sako da ya isar wa ‘yan Najeriya daga Buhari.
” Sannan Kuma Buhari ya koka kan yadda gwamnatocin baya suka rika warwason dukiyar kasarnan kamar naman farauta.
Atiku ya kara da cewa gazawar Buhari da rashin kwarewar sa wajen jan ragamar mulkin kasa da saita tattalin arziki ya fito karara inda ya furta da bakin sa cewa a karkashin sa tattalin arzikin kasar nan ya durkushe.
” Duk shugaban da zai iya fadin haka kai tsayi kwanaki kadan kafin zabe na nuna cewa ya gaza ne ya na neman yayi amfani da wannan dama domin karkato da fuskokin ‘yan kasa don jingina gazawar sa ga haka.
” Amma kowa ya sani an ci bakin wuya a karkashin wannan mulki da Buhari sannan talauci sai kara yawa yake a tsakanin mutanen kasa. Buhari yaga babu mafita sannan gazawar sa ya fito fili karara ne ya sa kawai ta hakan ne zai bullo a tausaya masa.
Shua’aibu Phrank da ya fitar da wannan sako na Atiku ya ce yanzu ‘yan Najeriya sun waye kuma jiki magayi. Sun gane cewa Buhari da makarraban sa sun lafta wa ‘yan Najeriya karerayi ne kawai a 2015 amma yanzu kan mage ya waye.
Discussion about this post