INNA RUTUTU: Gobe Talata za a haifi jarirai 25,685 a Najeriya -UNICEF

0

Hukumar Tallafa Wa Kananan Yara Ta Duniya, wato UNICEF, ta bayyana cewa a na sa ran a gobe ranar Talata , wato ranar da za ta kasance ranar 1 Ga Janairu, 2019, za a haifi jarirai har 25,685 a cikin kasar nan.

Wakilin UNICEF a Najeriya, Pernille Ironside ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) wannan hasashen albishir da hukumar ta yi a yau Litinin a Abuja.

Ironside ya ce wadannan adadin jarirai da za a haifa a Najeriya, su ke adadin kashi 6.5 na yaran da ake hasashe har su 395,072 da za a haifa daga cikin talatainin daren yau zuwa wayewar gari gobe Talata a fadin duniya.

Ya ce wadanda za a haifa gobe a Najeriya za su kai kashi 40 bisa 100 na daukacin jariran da za a haifa a fadin Nahiyar Afrika a gobe Talata.

Share.

game da Author