Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida da aka fi sani da Hukumar FIRS, ta bayyana tara kudade har naira tiriliyan 4.63 tsakanin Janairu zuwa Nuwamba, 2018.
Haka FIRS ta bayyana a ckin rahoton da ta mika wa Ma’aikatar Harkokin Kudade ta Tarayya.
Takardun bayanan sun nuna wadanda ta mika wa Kwamitin Rabon Kudaden Kasafin Ga Gwamnati, sun shigo hannun PREMIUM TIMES.
Hakan ya na nuni da cewa an samu kashi 72.6 bisa 100 na adadin kudaden shiga da aka yi kirdadon cewa za a tara a cikin shekarar 2018.
An tara naira tiriliyan daya daga harajin da ya danganci man fetur, wato PPT, sai kuma harajin da ake dora wa cinikin da kamfanoni ke yi, inda aka tara har naira tiriliyan 1.01, wato CIT.
Akwai kuma harajin VAT, wanda ake dora wa kowane dan Najeriya da ya yi ciniki a shagunan zamani, kantina, banki ko gidajen saida abinci inda aka tara naira bilyan 776.5 daga kayan da ake sarrafawa a cikin kasa.
Sai kuma naira bilyan 223.8 da aka tara daga harajin VAT kan kayan da aka shigo da su.