HARKALLAR GANDUJE: SERAP ta maka Buhari kotu, ta ce a tilasta shi ya binciki Ganduje

0

Kungiyar Kare Hakki da Tabbatar da Bin Turbar Doka da Ka’idoji (SERAP), ta maka Shugaba Muhammadu Buhari kotu, inda ta nemi kotu ta tilasta wa Buhari ya binciki Gwamnan Jihar Kano, Adullahi Ganduje.

SERAP ta nemi Shugaba Buhari ya umarci Ministan Shari’a Abubakar Malami da duk wata hukumar yaki da cin hanci, rashawa da wawurar kudade su binciki Ganduje, wanda aka fallasa a harkallar karbar toshiyar baki da kashe-mu-raba a cikin faya-fayen bidiyo da dama.

Dama a baya cikin watan Nuwamba, ta nemi Buhari ya sa a binciki Ganduje, kuma idan an same shi da laifi, to a hukunta shi.

Ta kuma nemi a tabbatar da an kare rai da lafiyar dan jaridar da ya fallasa Ganduje da iyalin sa, wato Jaafar Jaafar, Babban Editan Jaridar Daily Nigerian.

A cikin fushi SERAP ta ce ana neman raina wa ‘yan Najeriya wayau da hankali, domin har yau Buhari bai dauki matakin komai ba, kuma Majalisar Kano da ta fara binciken, ita ma ta watsar.

Ganin haka sai SERAP ta maka kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos. Karar mai lamba FHC/L/CS/2055/58, an shigar da ita ne ranar Juma’a, ta nemi kotu ta isar da umarni na gar-da-gar ga Shugaba Buhari ya umarci a fara binciken Ganduje.

SERAP ta ce ta shigar da wannan kara ce ba don son ran ta ba, sai domin abu ne muhimmi da ya shafi aikin gwamnati, aiki da gaskiya, da kuma tabbatar da an yi aikin gwamnati a kan ka’ida tare da bai wa hakkin shari’a adalcin ta.
SERAP ta ce idan Buhari ya bayar da wannan umarni, babu wani abu da zai yi asara.

Lauyan SERAP Bamisope Adeyanju ne ya shigar da kara a madadin kungiyar, a bisa la’akari da cewa Ganduje ya kantara laifi a karkashin dokar kasa ta 15 a Sashe na 5 na dokar 1999.

Ta kuma koka da yadda gwamnoni ke amfani da damar su suke tsula tsiya a lokacin da suke kan mulki.

Shi ma Ministan Shari’a, inji SERAP ta ce dokar kasa ta Sashe na 174 ta ba shi ikon bincikar zargin wawurar kudade da ake yi wa Ganduje.

Ba a dai sa ranar da za a fara sauraren karar ba.

An sha sukar Buhari wajen kauda kai daga binciken wadanda ake zargi dac aikata laifi a karkashin gwamnatin sa.

Cikin su har da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, Shugaban APC, Adams Oshiomhole, Babachir Lawal, Abba Kyari, Akpabio da ya koma APC da Nuruddeen Obanikoro da shi ma ya koma APC da sauran su da dama.

Jam’iyyar Adawa na korafin cewa ita kadai ake yi wa ‘ya’yan ta bi-ta-da-kulli. Har su na buga misali da Ganduje cewa da gwamnan PDP ne da yanzu Buhari ya rika buga misalin cin hanci da rashawa da shi.

Share.

game da Author