Har yau ba a kwaso gawarwakin ‘yan sandan da maharan Zamfara suka kashe ba

0

Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda da ke Abuja ta ki yin karin hasken bayar da takamaimen yawan ‘yan sandan da mahara suka kashe a Zamfara, a ranar 29 Ga Nuwamba.

An hakkake cewa an kashe akalla ‘yan sanda 50 daga cikin jami’an tsaron da aka tura jihar domin fatattakar masu hare-hare a jihar, kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar daga majiyar ta.

Kwanaki uku bayan kisan, duk da cewar iyalan mamatan da aka kashe daga ‘yan sandan su damu da jin halin da ‘yan uwa da iyaye da mazajen su ke ciki, har yau hukumar ‘yan sanda ba ta yi bayanin komai ba.

Wasu da abin ya fi shafa daga cikin iyalai da jami’an ‘yan sanda, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun shirya kwaso gawarwakin ‘yan uwan na su kuma za su kwaso wadanda aka ji wa ciwo a cikin dazukan.

“Tuni har gawarwakin su fara rubewa, saboda ba mu da halin zuwa mu kwaso su.” Haka wani jami’in dan sanda ya shaida wa PREMIUM TIMES, amma kuma ya ce a sakaya sunan sa.

“Mu na sane da cewa wadanda aka kashe din sun zarce 50.”

Jami’in dan sandan ya ce masu harin sun yi kwanton-bauna a cikin yankunan, sannan kuma jami’an leken asiri sun nuna cewa idan ‘yan sanda suka sake yunkurin shiga dajin domin kwaso gawarwaki da kuma ceto sauran wadanda suka ji raunuka, to akwai yiwuwar sake afka musu ta inda ba su sani ba.

An tabbatar da cewa shi kan sa Habila Joshak shugaban gagarimin sabon shirin da ‘yan sanda suka yi a yankin, ya isa cikin dajin a bisa helikwafta, sai dai kuma ya kasa sauka a kasa, saboda mahara sun bude masa wuta daga kasa. An ce hakan ne ta sa tilas sai dai ya gama shawagi a sama, ya koma Gusau.

“Kai su kan su sojojin kasa ma ba za su iya shiga cikin surkukin jejin ba. Mun ji an ce za su kawo sojojin sama domin su je su ratattaka wa maharan wuta daga sama, sannan a samu damar kwaso matattun da ‘yan sandan da suka ji rauni.” Haka wani dan sanda ya bayyana wa PREMIUM TIMES, kuma ya roki a sakaya sunan sa.

Kakakin ‘yan sanda bai bayar da amsar da PREMIUM TIMES ta yi masa ba. Amma ranar Juma’a sai kakakin, Jimoh Moshood ya bada sanarwar cewa ‘yan sanda sun kashe mahara 104 a Zamfara, kuma ya ce an kone mabuyar su har wurare 50.

Ya ce an kuma kwato shanu da tumakan da suka sace daga hannun jama’a.

Sai dai kuma jim kadan bayan samarwar da Moshood ya yi, wasu manyan jami’an ‘yan sanda sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an kashe jami’an su da dama a Zamfara.

Wasu kuma sun nuna cewa kamata ya yi tun a ranar Juma’a Sufeto Jamar na Yan Sanda, Ibraheem idris ya bayyana hakikanin yawan wadanda aka kashe da kuma irin kokarin da kae yi domin kwaso gawarwakin su da kuma ceto wadanda aka ji wa raunuka.

“Wadanda aka kashe din nan fa duk kananan ‘yan sanda ne. Amma sai a yi tunain cewa su ma fa mutane ne kamar kowa. Ko an bayyana ko an boye, wata rana dai gaskiya za ta bayyana cewa an kashe su.”

“Rayukan ‘yan sanda sun fi na mahara muhimmanci, amma sai ga shi Sufeto Janar ya bari an fadi yawan mahara da aka kashe, An ce 104, amma kuma har yau an kasa fadin yawan ‘yan sandan da aka kashe a kan aikin su na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Zamfara.” Inji wata majiyar.

Share.

game da Author