Har yanzu ’Yan Agajin mu su 20 na hannun masu garkuwa da mutane – Kungiyar Izala

0

Kungiyar Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), ta bayyana cewa har yanzu akwai mambobin kungiyar agaji na Izala da masu garkuwa da mutane suka tsare a cikin dajin Jihar Katsina.

Shugaban Kungiyar Izala Bangaren Jos, Sheikh Sani Yahaya ne ya bayyana cewa ana tsare da su ne tun a ranar 23 Ga Disamba, a cikin dajin Karamar Hukumar Jibiya da ke Jihar Katsina.

Sani Jingir ya bayyana wa manema labarai haka a wani taro da ya yi da su jiya Lahadi a hedikwatar kungiyar da ke Jos.

Ya ce an sace ne a kan hanyar su ta komawa Sokoto, bayan sun halarci taro a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.
Ya ce an sace su ne yayin da ya rage saura kadan su shiga jihar Zamfara.

“Masu garkuwa da mutane sun tsayar da su a cikin lumana. Daga nan suka tattara su gaba daya, suka yi cikin daji da su, suka bar motar da suke ciki a kan titi.” Inji Sani Jingir.

Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari kira shi ta waya, inda ya jajanta masa kama ‘yan agajin da aka yi.

Da aka tambaye shi ko masu garkuwar sun tuntubi kungiyar Izala, sai ya ce har zuwa yanzu dai ba su tuntubi kowa ba.

A karshe ya roki masu garkuwar su ji tsoron Allah su saki ‘yan agajin, domin aikin taimako su ke yi, ba wanda ke biyan su albashin ko sisi.

Har yanzu su ma ‘yan sanda ba su yi magana a kan batun sace ‘yan agajin ba.

Share.

game da Author