Gwamnatin tarayya ta hana siyar da maganin hawan jini ‘Valsartan’

0

Hukumar (NAFDAC) ta bayyana cewa daga yanzu gwamnati ta hana shigowa da siyar da maganin hawan jini ‘Valsartan’.

NAFDAC ta bada wannan sanarwa ne ranar Talata a shafinta na yanar gizo inda ta bayyana cewa maganin Valsartan magani ne da masu fama da cutar hawan jini ke amfani da shi domin samun sauki.

Hukumar ta bayyana cewa gwamnati ta yanke hukuncin haka ne bisa ga sakamakon binciken da hukumar binciken magungunan (MHRA) ta gano cewa maganin na dauke da guba da ka iya cutar da lafiyar mutane.

Bayanai sun muna cewa sinadarin nitrosodimethylamine (NDEA) na kawo cutar dajin dake kama hanta tare da cutar da sauran kayan ciki dake jikin mutum.

NAFDAC ta yi kira ga likitoci da mutane su guji amfani da wannan magani sannan su gaggauta kai maganin ofishin NAFDAC mafi kusa da su.

Share.

game da Author