Gwamnatin Najeriya ta maida wa Saraki martanin furucin sa cewa ‘babu alfanu’ a Kasafin 2019

0

Gwamnatin Tarayya ta maida wa Shugaban Majalisar Dawatta Sanata Bukola Saraki martani, bayan ya yi ikirarin cewa kasafin 2019 ba shi da wani alfanu a cikin sa.

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana haka jiya Juma’a ga manema labarai a Fadar Gwamnati, Aso Villa.
Lai ya ce gwamnatin tarayya ba za ta ba ta bakin tsayawa ta na sa-in-sa da Saraki ba.

Ya kara da cewa shi da bangaren zartaswa na gwamnati ya sauke nauyin da ke kan sa na kasafin kudi, tunda har ya tsara, kuma an gabatar wa majalisa.

An ruwaito Saraki na cewa kasafin ba shi da wani tasiri idan aka yi la’akari da kudaden shigar da ake samu da kuma sauran mishkilolin da ke tattare da tafiyar da gwamnati da kuma abubuwan da suka shafi tattalin arzikin kasa.

Haka jaridar Vanguard ta ruwaito Saraki ya fada a matsayin sa na dan adawa, dan jam’iyyar PDP kuma Daraktan Kamfen na Yakin Neman Zaben Atiku Abubakar.

Lai ya ce ba za su tsaya sa-in-sa da majalisa ko Saraki ba, tunda su dai a na su bangaren sun yi iyakar yin su, kuma sun yi bakin kokarin su na gabatar da kasafin kudi daidai karfin tattalin arzikin Najeriya.

“Yanzu ya rage ga majalisa ita kuma ta yi na ta aikin a kan kasafin kudin.”

Lai ya ce gwamnatin Buhari ta cika dukkan alkawurran da ta dauka.

Daga nan ya yi wa kowa fatan kallama bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara lafiya lafiya.

Share.

game da Author