Gwamnatin Najeriya na kauda kai daga hukunta sojoji da ‘yan Boko Haram da suka yi kisan gilla – AI

0

Kungiyar Jinkai ta Duniya, wato Amnesty International, ta yi kira ga Kotun Kasa-da-kasa ta duniya, ICC, da ta gaggauta binciken zargin kisan gilla da tauye hakkin dan Adam da sojojin Najeriya da Boko Haram kan yi, amma gwamnatin na juya baya ba ta damu da yin kowane irin hukunci da ya kamata ta dauka ba.

Daraktan Bincike na hukumar, Netsanet Belay, ya ce za su yi binciken ne tunda gwamnatin Najeriya ta ki yin komai a kai.

Ya ce bincike ko shari’ar da ake yi wa Boko Haram, bulkara ce kawai, kuma abin takaici, domin ba a yin la’akari da irin take hakkin dan adam da kungiyar ta yi.

Sai kuma ya nuna takaicin sa dangane da wata shari’ar da aka yi wa wasu gungun ‘yan Boko Haram a cikin watan Oktoba na bara, 2017 cewa harigido ce, domin har yau ba za a iya gabe ceewa sun aikata laifi ba.

Ya ce irin wannan shari’a ana yin ta dai ne kawai, don kada a ce ba a yi komai ba.

Share.

game da Author