Gwamnatin jihar Jigawa za ta fara ciyar da daliban firamare daga aji 4 zuwa 6 na makarantun jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Ibrahim Hassan ya sanar da haka a taron wayar da kan masu fada a ji a fannin ilimin jihar game da shirin da gwamnati ke yi domin ciyar da daliban makarantun firamaren jihar da aka yi a Kaugama ranar Talata.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta sanr da fara ciyar da daliban firamaren jihar.
Bisa ga shirin gwamnati za ta ciyar da daliban firamare daga aji daya zuwa aji uku da suka kai 726,033.
Sauran da suka rage wato daliban aji 4 zuwa 6 kuma gwamnatin jihar zata ciyar dasu.
” Mun yi hayan kwararrun ma’aikata mata da za rika girka wa daliban abinci cikin tsafta.”
Bayan haka jami’in dake kula da shirin ciyar da daliban firamare abinci Bala Chamo ya yi kira ga matan da aka dauka da su tabbatar sun tafiyar da aiyukkan su cikin gaskiya.
A karshe shugaban karamar hukumar Kugama Ahmed Yahaya-Marke ya bayyana cewa karamar hukumar sa za ta hada hannu da gwamnatin tarayya da jiha domin ganin mutanen karamar hukumar sun ci amfanin dimokardiyya.