Gwamnati za ta fara kula da tsoffin kasar nan – Buhari

0

Gwamnatin tarayya za ta samar da fannin da zai rika kula da tsuffi a asibitocin Najeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da haka a taron masana a Abuja.

Buhari ya bayyana cewa gwamnati ta amince ta yi haka ne domin samar da kiwon lafiya mai nagarta kuma kyauta ga mutanen Najeriya.

” Muna da sanin cewa wasu jihohi a kasar nan na ba yara ‘yan kasa da shekara biyar da mata magani kyauta sannan mu kuma yanzu zamu karfafa haka ta hanyar samar da kula wa tsofaffi a kasar nan kauyta.

Sannan ya kuma yi kira ga ma’aikatar kiwon lafiya ta tarraya kan gaggauta fara amfani da wannan shiri na kula da kiwon lafiyar tsofaffi.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne shugaban kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya da suka kware wajen kula da matsalolin da ya shafi tsufa a Najeriya (GAN) Usaman Ahmed ya yi kira ga gwamnati kan ware kudade domin yi wa tsofaffin kasar nan hidima.

Ahmed ya yi wannan kira ne ganin cewa ire-iren wadannan matsaloli ya faskara a kasar nan.

Ya ce a yanzu haka tsofaffi miliyan tara ne suke a kasar nan sannan babu isassun ma’aikata da wuraren kula da su da gwamnati ta kebe domin su.

” Bincike ya nuna cewa adadin yawan tsofaffin dake kasar nan za su fi haka yawa kafin nan da shekara 2050.”

Ahmed yace kara yawan ma’aikata, kara yawan asibitoci da wuraren kula da tsofaffi na cikin matakan da ya kamata gwamnati ta dauka cikin gaggawa.

Share.

game da Author