Shugaban hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau na kasa (NACA) Sani Aliyu ya bayyana cewa gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu sun bude asusu domin tara kudi don tallafa wa masu fama da cutar kanjamau a Najeriya.
Aliyu ya sanar da haka ne a taron wayar da kan mutane game da cutar kanjamau da aka yi a Abuja.
Ya bayyana cewa sun tara dala miliyan 15 a wannan asusu sannan suna sa ran cewa sauran kungiyoyi masu zaman kansu za su bada nasu gudunwamar.
Aliyu ya ce gwamnatin jihohi sun sanar cewa daga yanzu za su fara ware kashi daya daga cikin kudaden da suke karba daga gwamnatin tarayya domin tallafa wa masu fama da cutar.
Idan ba a manta ba mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnati a shirye take domin ware isassun kudade domin dakile yaduwar cutar kanjamau a kasar nan.
Osinbajo ya sanar da haka ne a taron ranar cutar kanjamau na shekarar 2018 a Abuja mai taken ‘kusan matsayin ku game da kanjamau’.
A wajen taron Osinbajo ya bayyana cewa burin gwamnati shine ta ga cewa ta sami nasarar kawar da cutar nan da shekarar 2030 kwata-Kwata a Najeriya
” Gwamnati na kokarin ganin ta samar da isassun maganin dakile yaduwar kanjamau sannan tana kokarin ganin ta kara mutane akalla 50,000 da suke dauke da cutar cikin adadin yawan mutanen dake dauke da cutar da gwamnati ke kula da a kasar nan.
Ya kuma ce ya na sa ran cewa sakamakon kidayar yawan mutanen dake dauke da cutar da hukumar hana yaduwar Kanjamau ta Kasa (NACA) ke gudanar wa zai taimaka wa gwamnati wajen tsara hanyoyin da suka fi dacewa wajen kawar da cutar a Najeriya.
Bayan haka ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya hori mutane da su rika zuwa yin gwajin cutar domin sanin matsayi domin hakan zai taimaka matuka domin ganin an dakile yaduwar cutar.
” Bincike ya nuna cewa kashi 30 bisa 100 na mutanen kasar nan ne ke da masaniya game da matsayin su game da cutar.
A karshe shugaban hukumar NACA Sani Aliyu ya jinjina wa kungiyoyin bada tallafi na kasar Amurka, Bankin Duniya da sauran su bisa ga goyan bayan da suka ba hukumardon hana yaduwar cutar.
Ya ce NACA za ta gabatar da sakamakon kidayar da take gudanarwa nan da watan Maris din 2019, sannan yana sa ran cewa sakamakon zai taimaka wa gwamnati wajen dakile aduwar cutar a Najeriya.
Sannan kuma idan ba a manta ba ” Bincike ya nuna cewa daga cikin mutane miliyan 2.1 dake dauke da cutar kanjamau a kasa Najeriya, 240,000 matasa ne masu shekaru 10 zuwa 24.
Discussion about this post