Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara Ibrahim Wakkala ya koka kan yadda gwamman jihar AbdulAziz Yari ya maida shi saniyar ware a harkokin mulki a jihar.
Wakkala ya bayyana wa manema labarai a garin Gusau cewa gwamna Yari ya yi watsi da shi ya maida shi saniyar ware a harkokin gwamnati.
” Babban laifin da nayi shine fitowa takarar gwamna da na yi wanda doka ce ta bani wannan dama. Ko kuwa akwai inda doka tace kada in yi takarar gwamna don ina mataimakin gwamna mai ci. Wannan shina ya sa gwamna Yari ya yi watsi da ni kwata-kwata da hatta alawus-alawus dina dana ma’aikatan ofishina ma ba a bani yanzu.
” Sannan kuma ko muka wa kakakin majalisar jihar ragamar mulki da gwamna yayi bai dace ba sannan saba wa doka ce domin doka cewa ta yi sai in babu mataimakin gwamna ne za a iya mika wa wani ragamar mulkin jiha idan babu gwamna.
Darrktan yada labaran Wakkala, Yusuf, ya bayyana cewa a kullum Wakkala na Ofishin sa ya na aiki, amma kuma zama ne kawai yake yi babu abin da yake yi na aiki saboda maida shi saniyar ware da aka yi.
Da aka nemi ji daga bakin gwamna Yari, cewa yayi wannan magana ba shine a gaban sa ba, abinda ke gaban sa shine ya ga an dawo da zaman lafiya da tsaro a jihar.