Gidauniyyar Bill da Melinda Gates ta koka kan karancin kudi da ake ware wa fannin kiwon lafiya a Najeriya

0

Gidauniyyar Bill da Melinda Gates ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara yawan kudaden da take ware wa fannin kiwon lafiyar kasar domin samar da kiwon lafiya mai nagarta ga mutanen kasar.

Gudauniyyar ta yi wannan kira ne a taron inganta hanyoyin samar da dabarun bada tazarar iyali da cibiyar DRPC ta shirya sannan ta gudanar babban birnin tarayya, Abuja ranar Laraba.

Jami’ar gidauniyyar Paulin Basinga ta bayyana cewa yin hakan zai taimaka wajen karkato da hankalin gwamnatin kasar wajen inganta kiwon lafiyar mutane da hana kasar yawan dogaro da tallafin da take samu daga kasashen waje musamman yanzu da suka fara janye tallafin.

” Sanin kowa ne cewa idan ana so kasa ta ci gaba dole sai kasar ta sami shugabanin masu kishi da za su tabbatar cewa mutanen su na samun kiwon lafiya mai nagarta da kuma ilimi.

A karshe Basinga ta ce samar da dabarun bada tazarar iyali zai taimaka wajen kawar da matsalolin da mata da kuma jarirai kan fuskanta na yawan mace-mace a wasu lokutta da dama saboda rashin kula da ba a baiwa fannin kiwon lafiya.

A dalilin irin haka ne cikin irin gudunmawar da Najeriya kan samu daga kungiyoyin duniya Jami’in kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Wondimagegnehu Alemu ya bayyana cewa kungiyar ta ware dala miliyan 178 domin tallafawa Najeriya wajen kawar da wasu cututtuka har na tsawon shekaru biyu.

A bayanan da ya yi Alemu ya ce za a kashe dala miliyan 127 wurin kawar da cutar shan inna, Za kuma a kashe dala miliyan 30 wajen kawar da cututtukan da aka fi kamuwa da su a kasar kamar su zazzabin cizon sauro, tarin fuka da cutar Kanjamau.

Ya kuma kara da cewa dala miliyan 8.1 kuwa za a kashe su wajen inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana sannan da dabarun bada tazarar haihuwa sannan sauran kudaden za a yi amfani da su ne wajen hana bullowar cututtuka a kasar.

Share.

game da Author