Tsohon shugaban kasar Amurka George HW Bush ya rasu ranar Juma’a.
Kamar yadda iyalan marigayin suka sanar a shafin su na tiwita sun bayyana cewa, Bush ya rasu yana da shekaru 94.
Bush dai shine ya jagoranci yakin da kasar Amurka ta yi da kasar Iraqi a 1994.
Ya rasu yana da ‘ya’ya 5, jikoki 17 da tattaba kunne 8.
Bush ya fi kowane tsohon shugaban kasar Amurka dadewa a duniya sannan kuma daya daga cikin yayan sa biyar, George Bush shima yayi shugabancin Amurka bayan Clinton.
Discussion about this post