Hukumar Tsaro ta Sojoji ta gargadi Zaratan Musamman da aka horas domin yaki da Boko Haram cewa su nuna wa duniya sun fi Boko Haram sanin makamar yaki da kuma kwarewa wajen yin nasara a kan abokan gaba.
Babban Hafsan Hafsoshin Sojoji, Janar Tukur Buratai ne yay i wannan horon Jiya Lahadi ga Zaratan Musamman na a-yi-ta-ta-kare na Special Forces da kuma zaratan gumurzu na Strike Group da aka jibge a Arewa maso Gabas.
“An tsamo ku ne musamman domin a kawo ku nan yankin Arewa maso Gabas. Kuma ba a banza a ka ba ku hoto ba, an koya muku dabarun iya yaki ne na musamman, shi ya sa ma ake kiran ku Zaratan Musamman.
“Na zo ne domin na shaida musu cewa akwai babban aiki kuma muhimmi da aka dora muku. Don haka ya zama dole ku aiwatar da shi ta yadda ya dace.”
Buratai ya hore su cewa an kai su ne domin su nuna bambancin cewa ruwa fa ba sa’ar Kwando ba ne.
Ya ce idan ma a baya an samu wani cikas ko kalubale, to a yanzu ne za a kawar da wannan cikas ko kalubalen, kuma su ne za su kawar da shi.
Buratai ya kuma gargade su cewa yaki suka je yi ka’in da na’in, babu tsoro.babu razana kuma babu fargaba. Ya na mai cewa aikin soja ba na masu zuciyar zakara da zabo ba ne.
Discussion about this post